Rasha ta shirya daftarin dakile Shirin turai na mayar da takunkumin MDD kan Iran

Rasha ta tabbatar da tsara wani daftarin kudiri a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da nufin hana duk wani yunkuri na dawo da takunkuman

Rasha ta tabbatar da tsara wani daftarin kudiri a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da nufin hana duk wani yunkuri na dawo da takunkuman MDD kan Iran da ke da alaka da batun shirinta na nukiliya, da ake kira da “snapback”.

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Dmitry Polyanski ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani taron ‘yan jaria a wannan Talata.

Kasashen Turai uku na Birtaniya, Faransa, da Jamus  abokan kawancen Amurka a yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, sun yi ta kokarin ganin an dawo da matakan kakaba wa Iran takunkumai bisa hujjar cewa bata yi aiki da yarjejeniyar ba kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

Wakilin na Rasha ya ce, duk da haka “Rasha da Sin suna son ba da sarari domin yin amfani da hanyar diflomasiyya tare da samar da wasu damammaki don neman mafita ta hanyar siyasa kan wannan batu.”

Ya ce Moscow da Beijing suna yin hakan ne a matsayinsu na “mambobin da ke da alhakin aiwatar da shirin na hadin gwiwa ko kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka fi sani da  (JCPOA).

A shekara ta 2018, Amurka ta fice daga yarjejeniyar a wani mataki da ya sabawa doka da ka’ida ta kasa da kasa, tare da mayar da wasu takunkumanta a kan kasar ta Iran.

A nasu bangaren Kasashe uku na Turai Birtaniya, Faransa, da Jamus  ba wai kawai sun gaza cika alkawarin da suka dauka ba ne,  har ma sun bi sahun Washington ne ta hanyar mayar da nasu takunkumin da kokarin kawo cikas da yin tarnaki ga duk wasu harkokin tattalin arziki da suka shafi kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted