A yau asabar ce dubban mutane daga ciki da wajen kasar iran suka taro a hubbaren Imam Aliyu dan Musa Arredha, da ke birnin Mashad a arewa maso gabacin kasar Iran don tunawa da ranar shahadarsa a karshen watan Safar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Imam Reza (AS) shi ne Limami na 8 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma hubbarensa na daga cikin wurare masu tsarki a wajen shi’a Imamiyya a ko ina suke a duniya. Miliyoyin musulmi ne suke zuwa hubbarensa don addu’a’oii da kuma girmama shi.
Shahadar Imam Reza (a) dai, ya kasance a shekara ta 203 HK. A lokacinda sarki Ma’amoon daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya shayar da shi guba. Imam Aliyu dan Musa Arridha (a) yana daga cikin liamai 12 wadanda manzon All..(s) ya barwa musulmi a matsayun wasiyoyinsa har duniya ta nade.