Gwamnatin korea ta Arewa ta yi tir da Korea ta kudu saboda harbe-harben takala ba tare da wani dallili ba.
Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Korea ta kudu na tabbatar da labarin. Ta kuma kara da cewa sojojinta sun yi harbe-harben gargadi ne saboda shiga yankin kasar wanda sojojin Korea ta Arewa suka yi a makon da ya gabata.
Babban hafsan sojojin Kasar Korea ta Kudu Lt. Gen. Ko Jong Chol.a birnin ko Seoul: ya ce sojojin sun tsallaka kan iyakar kasashen biyu, wanda ya sa sojojimmu suka yi harbin gargadi, sai kuma suka yi arewa suka koma cikin kasarsu.
Wannan rigimar ta sa koreoyoyin biyu suka kara toshe hanya tilo wacce ta hada kasashen biyu.
Kasashen biyu dai basu taba samun zaman lafiya bat un lokacin kafasu, bayan yakin duniya na biyu.