Rundunar Sojin Yaman ta sanar a jiya Juma’a cewa, dakarunta sun kai wani hari da makamai masu linzami a kan filin sauka da tashin jiragen sama na Ben Gurion da ke yankin Jaffa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye kuma take kiran yankin da Tel Aviv a yanzu.
A cikin sanarwar, kakakin rundunar sojan kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa makamin ya ratsa na’urorin tsaron sararin samaniyar Isra’ila tare da samun nasarar isa wurin da aka saita shi. Ya yi nuni da cewa, harin ya haifar da rudani a tsakanin makiya, wanda ya tilasta wa miliyoyin yahudawa ‘yan share wuri zauna tserewa zuwa wurare na karkashin kasa, kuma ya kai ga dakatar da dukkanin ayyukan filin jirgin.
Ya kara da cewa sojojin saman sun gudanar da ayyukan soji guda biyu ta hanyar amfani da jirage marasa matuka, inda suka nufi wasu muhimman wurare biyu na sojin Isra’ila a Jaffa da Ashkelon, yana mai tabbatar da cewa dukkan hare-haren biyu sun cimma nasara.
Ya bayyana cewa wadannan hare-hare wata hanya ce ta nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da ake zalunta, da kuma mayar da martani ga laifukan kisan kiyashi da jefa al’ummar zirin Gaza a cikin matsananciyar yunwa.
Saree ya kammala bayaninsa da tabbatar da cewa: “Yemen tare da al’ummarta , da sojojinta da kuma jagororinta na gaskiya, suna tare da al’ummar Gaza, kuma wadannan hare-hare za su ci gaba har sai an kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da kuma kawo karshen killace yankin baki daya.