Pezeshkiyan: Iran Tana Sun Zaman Lafiya Da Dukkan Kasashen Duniya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kasarsa tana son zaman lafiya da dukkan kasashen duniya, tare da amincewa da kuma mutunta kaniyakokin da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kasarsa tana son zaman lafiya da dukkan kasashen duniya, tare da amincewa da kuma mutunta kaniyakokin da aka shatwa ko ko wace kasa.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a ranar Laraban da ta gabata a kasar Belarus inda ya kai ziyara na kwanaki.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda yana ganawa da Iraniyawa mazauna kasar Belarus. Ya bayyana amfanin Iraniyawa a kasashen wajen, Sannan ya yaba Iaraniyawa masu zama kasar Belarus, ya bayyana cewa zabi ne mai kyau, a matsayin kasar zama, ya kuma yi fatan za su zama jakadan kasar Iran masu bayyana halaye masu kyau kamar yadda ya dace.

Da ya sake dawowa a kan maganarsa ta Farko shugaban yace wasu manya-manyan kasashen duniya suna sun hana kasar Iran ci gaba da take samu a bangarorin ilmi da dama.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted