Iran Ta Yi Tir Da Sabbin Takunkuman Tattalin Arzikin Da Burtaniya Ta Dora mata

Ofishin jakadancin kasar Iran a birnin London ya fidda sanarwan yin tir da sabbin takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Burtaniya ta dorawa daddaikun Iraniyawa

Ofishin jakadancin kasar Iran a birnin London ya fidda sanarwan yin tir da sabbin takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Burtaniya ta dorawa daddaikun Iraniyawa da kuma wasu kamfaninoni. Sanarwan ta kara da cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma nuna kiyayya ne ga kasar. Don haka Iran tana kira ga kasar Burtania ta kawo karshen kiyayya da take nunawa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa takunkuman sun shafi fitattun Iraniyawa da kuma wasy kamfanoni, kuma yin hakan zai iya shafar dangantakan diblomasiyyar kasashen biyu.

Gwamnatin kasar Burtaniya ta ta sha dorawa JMI takunkuman tattalin arziki, tun farkon juyin juya halin musulunci a shekara 1979 har zuwa fiye da shekaru 46. Takunkuman tattalin arzikin sun hada da na Banki, man fetur tsaro  da suransu, bayan sanarda yarjeniyar shirin nukliyar kasar Iran a shekara ta 2015 wato JCPOA, Burtaniya ta dauke takunkuman na wani lokaci sai ta sake dawo da su tare da hadin kai da sauran kasashen Turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted