Iran ta yi Allah-wadai da takunkumin Amurka a kan alkalan kotun ICC

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah-wadai da sabon takunkumin da Amurka ta kakaba wa alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta ICC yana

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah-wadai da sabon takunkumin da Amurka ta kakaba wa alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta ICC yana bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na boye laifukan yakin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a Falasdinu da kuma cin zarafi ga shari’ar kasa da kasa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba wa wasu alkalan kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC a matsayin wani babban laifi da kuma cin zarafin bil’adama, da halasta kisan kare dangi a Falasdinu.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Baqaei ya ce, “Kakaba takunkumin da Amurka ta yi kan karin wasu alkalan kotunan ICC guda hudu (na kasashen Canada, Senegal, Fijian, Faransa) saboda bin kadun shari’ar laifukan ta’addancin Isra’ila, hakan ba wai kawai ya zubar da mutunci na shari’a ba ne, hakan ma a kansa yana matsayin laifin yaki.”

Ya kara da cewa, “Wannan farmaki kan alkalan kotun ICC, yana a matsayin bayar da cikakken lasisi ne ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila domin ci gaba da aikata lisan kare dang ikan al’ummar Falastinu a Gaza da sauran yankunan Falastinawa da ta mamaye.

Baqaei ya ci gaba da cewa “Irin wannan haramtacciyar doka ta bayyana hakikanin tushen tsarin dokoki na Amurka’: tsarin rashin bin doka da wawantar da al’ummomin duniya da yin gaban kai wajen nuna karfa-karfa a kan raunana.” in ji Baqaei.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted