Iran Tana Ci Gaba Da Karfafa Ayyukan Tsaron Kasar

Ma’aikatar tsaron kasar Iran ta jaddada cewa: Ana ci gaba da karfafa ayyukan tsaron kasar ba tare da nawa ba A cikin wata sanarwa da

Ma’aikatar tsaron kasar Iran ta jaddada cewa: Ana ci gaba da karfafa ayyukan tsaron kasar ba tare da nawa ba

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ranar masana’antun tsaro na kasar Iran, ma’aikatar tsaron kasar Iran ta tabbatar da cewa: Makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fahimci cewa, duk wata kasada ko kuskure mummunan lissafi a yankin zai fuskanci mayar da kakkausar martani daga sojojin kasar Iran.

Bayanin ya ci gaba da cewa: Tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, da faduwar gwamnatin Shah mai samun goyon bayan kasashen waje, da kuma kawo karshen ikon sojan Amurka da suke ba da shawara kan harkokin sojojin Iran, kasar ta shiga wani sabon mataki na dogaro da kai da wadata a fagen masana’antar tsaro, duk da tsawon shekaru arba’in da Iran ta kwashe tana fuskantar rashin adalci da takunkuman zalunci, amma masana’antar tsaronta da kokarin kwararru da masana masu kishin kasa sun yi kokarin samar da gagarumin ci gaba da samun nasarori masu ban mamaki a wannan fagen.”

Ma’aikatar ta kara da cewa: Nasarorin da aka samu a fagagen makamai masu linzami, da makaman kariya, da sararin samaniya, da kuma kera nau’o’in na’urorin tsaro daban-daban bisa ka’idojin kasashen duniya na baya-bayan nan, sun mayar da kasar daga kololuwar rashin dogaro da kasashen ketare zuwa kololuwar wadatar da kai da karfin iko, kuma hakan ya sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama babbar hanyar karfi da kare kai a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted