Gwamnatocin Iran da Masar sun bayyana damuwarsu da shirin Natanyahu na kwace zirin gaza gaba daya da kuma sauyawa falasdinawa da suka rage wurare da karfi, saboda ginawa yahudawa matsugunai a yankin.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministocin harkokin wajen na kasar Iran Abbas Aragchi da kuma tokwaransa na kasar Masar Badr Abdullatyf suna fadar haka a zantawa ta wayar tarho a jiya Laraba.
Bangarorin biyu sun yi maganar ci gaba da kisan kiyashin da yahudawan suke a Gaza, da kuma musibar da suke fuskanta na karancin abinci da kisan da ake masau.
Kasar Iran dai ta bukaci taron kungiyar kasashen musulmi OIC a birnin Riyar na kasar saudiya a karshen watan Augusta da muke ciki don kara tattauna wannan batun.
Ya ce taron na Jidda dam ace ta kara daukar matakai ba ta baka kadai ba sai dai har na aikace don tallafawa falasdinawa a gaza.