Gagarumar zanga-zanga wanda daruruwan mutane suka gudanat a birnin São Paulo na kasar Brazil wannan ya hana jawabin jakadan HKI a karamin ofishinn jakadancin Amurka dake birnin., .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu zanga zanga sun hana jakadan shiga yalin da ofishin jakadancin Amurka ke kansa don gudanar da jawabinsa. Wannan ya nuna yadda al-amarin Gaza, ya game duniya gaba daya , yake kuma shafar wasu al-amuran gwamnatin gwamnatin Amurka.
Banda haka rikicin gaza, ya gama kan mutane da dama a duniya, ta yadda ba kasashen larabawa da musulmi abin ya shafa ba, mafi yawan mutane a kasashen duniya suna kyamar abinda HKI take aikatawa a gaza.
A kasashen laten Amurka da dama mutane suna kyamar abinda HKI take yi a gaza, kuma suna daukar matakai na zanga-zanga kawai a baya-bayan nan, sai dai a kasar Brazil al-amarin ya fi muni.
Wasu masu magana a zanga zangar na sao poullo sun bayyana cewa ba zasu bar jakadan yahudawa ya bayyana ra’ayin sahyohniyya a kan kasar Brazil ba).