Amurka Ta Dakatar Da Bawa Falasdinawa A Gaza Visar Shiga kasar

Gwamnatin shugaban Trump ta bada umurnin a dakatar da bawa Falasdinawa daga Gaza visar shiga Amurka, bayan da wata kungiyar wacce take goyon bayan HKI

Gwamnatin shugaban Trump ta bada umurnin a dakatar da bawa Falasdinawa daga Gaza visar shiga Amurka, bayan da wata kungiyar wacce take goyon bayan HKI ta gabatar da korafi kan cewa Falasdinawa da suka ji rauni da dama suna zuwa Amurka don jinyan raunukan da suka sami a asbitocin Amurka.

Jaridar ‘the nation’ ta kasar Amurka ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen Amurka na fadar haka a shafinta na X, ta kuma kara da cewa a halin yanzu an dakatar da bawa dukkan falasdinawa daga Gaza visar shiga Amurka. Sannan bayan an kammala bincike mai yuwa a bawa wasu yan kasan Visar, bisa aikin jinkai da kuma don jinya kawai.

Wasu kungiyoyin kare hakkin na Falasdinawa a Gaza, sun yi tir da wannan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka, sun kuma bayyana cewa a halin yanzun kuma zai yi masu wuya daukar falasdinawa musamman yara wadanda suka ji rauni ko suke bukatar gaggawa don ceto rayuwarsu daga halaka.

Kungiyar Falasdinawa ta ‘Palastinian Children’s Relief Fun’ ta bayyana cewa, wannan matakin zai cutar da yaran Gaza da dama, saboda rashin shigar da wasu yaran Amurka  zai sa su kasa warkewa kwata-kwata ko kuma sum utu. Don haka kungiyar ta bukaci Amurka ta sake lalen wadannan matakan da ta dauka kan Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted