Shugaban Iran na Shirin fara wata muhimmiyar ziyara a Armenia da Belarus

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk.

Ya kara da cewa, a ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban zai  kai, yana shirin tattaunawa da manyan hukumomin Armeniya da Belarus, kan hanyoyin da za a bi wajen fadada dangantakarsu, musamman a fannin kasuwanci, da kuma sanya hannu a kan takardun yarjeniyoyi a tsakaninsu.

Sanaei ya kara da cewa an shirya kai ziyara a kasashen Armenia da Belarus a karshen watan Yuni, amma aka dage.

Ya kara da cewa, an kuma gayyaci shugaba Pezeshkian don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da za a yi a kasar Sin a karshen watan Agusta.

Ziyarar ta Pezeshkian ta zo ne a daidai lokacin da Armeniya da Azabaijan suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranci kullawa, inda a karkashinta za a kafa wata hanyar sufuri da ta hada Azarbaijan da na Nakhchivan.

A karkashin yarjejeniyar da aka kulla a Washington a ranar 8 ga watan Agusta, Armenia ta bai wa Amurka hakki na musamman don samar da wata hanya a kudancin lardin Syunik, wanda ke kan iyaka da Iran.

Iran ta dade tana adawa da wannan ra’ayin, tana mai cewa za ta sauya tsarin siyasar yankin Kudancin Caucasus kuma zai takaita ikon Iran na amfani da hanyoyin sufuri a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted