Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu

An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar

An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana.

Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza.

Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya shiga yakin da ake yi a zirin Gaza ne a makonnin da suka gabata.

Wani bincike da sojojin mamayar Isra’ila suka gudanar, wanda aka buga sakamakonsa a ranar 3 ga watan Agusta, ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kashe kansu a cikin dakarunta, sun faru ne sakamakon yanayin fada a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted