Iran Ta Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashen Yankin

Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran

Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”. Wadannan kalamai tana nuna karara aniyar gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasashe masu cin gashin kansu da suka hada da Masar, da Jordan, da Lebanon da kuma Syria, tare da la’akari da su a matsayin babban misali na keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a safiyar yau Alhamis, Baqa’i ya yi ishara da yadda ake ci gaba da keta doka da kuma aikata munanan laifuka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta ke tafkawa, musamman ma mamaye yankunan Falasdinawa da kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a kan al’umma Falasdinu.

Baqa’i ya ci gaba da cewa: Amincewar da fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya yi na cewa yana da ”aiki na tarihi da na ruhi” don tabbatar da wannan muguwar tunani tun daga kogin Nilu har zuwa Fırat, wata shaida ce karara ta mulkin mallaka ta masu yanke shawarar wannan gwamnati ta miyagun al’umma da kuma kai hari kan ‘yantacciyar kasa mai ikon domin mamaye yankunan kasashensu, kuma wajibi ne a yi Allah wadai da wannan muguwar manufa ta tunanin mamaye yankunan kasashen musulmi daga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da  kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da dukkanin gwamnatoci, a matsayin wannan furuci na cin zarafi da keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin dokokin ƙasa da ƙasa.”

Iran

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted