Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba

Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan

Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba.

Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba.

Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa la’akari da yadda lamarin ke nuni da alamun  tada zaune tsaye, da kin amincewa da  zaman lafiya a yankin, da kuma dagewa kan ta’azzarar rikici.”

Sanarwar ta jaddada cewa, wannan lamari ya ci karo da muradun sassan yanki da na kasa da kasa masu son zaman lafiya da ke son cimma daidaiti ta fuskar tsaro da zaman lafiya ga daukacin al’ummomin yankin.

Ya jaddada cewa “babu wata hanya ta samun zaman lafiya sai ta hanyar komawa kan teburin shawarwari, kawo karshen yakin Gaza, da kafa kasar Falasdinu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted