Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace

Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron

Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo.

Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.”

Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu.

A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari da ake zargin Iran da tsoma baki a zaben Iraki Larijani ya ce: Al’ummar Iraki suna da hankali da jajircewa kuma ba sa bukatar wani takunkumi, inda ya kara da cewa a yau ya gudanar da taruka da dama a birnin Bagadaza, inda aka tattauna batutuwan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted