Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa kasar Lebanon tana da hakkin kare kanta, kuma tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don yin haka. Kumfanin dillancin labaran

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa kasar Lebanon tana da hakkin kare kanta, kuma tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don yin haka. Kumfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Bakae yana fadar haka a yau litinin ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Iran ta yi imanin cewa gwamnatin kasar Lebanon tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don kare kasar daga mamayar HKI.

Sannan ya kammala da cewa batun tsaron kasar Lebanon wani abu ne na cikin gida kungiyoyin siyasa da kuma gwamnatin kasar suna iya tattaunawa a tsakaninsu don zabar hanyar da ta dace don kare kansu daga makiyansu. Musamman HKI wacce ta sha kokarin mamaye kasar amma suka kasa. Kungiyar hizbullah ta hanasu shiga kasar. Amma duk da haka firai ministan kasar Nawaf Salam y ace sai an takaita rike makamai a kasar Lebanon zuwa ga gwamnati kadai .

A wani zaben raba gardama da aka gudanar a kasar ta lebanon ya nuna cewa mafi yawan mutanen kasar basu da ra’ayin kwance damarar kungiyar Hizbullah. Inda kasha 54% suna son hizbullah ta rika makamanta a yayunda 46 suna son a kwance damarata. Firai ministan HKI dai ya bayyana a fili kan cewa gwamnatin kasar Lebanon ta yi masa aiki saboda kwance damar kungiyar Hizbullah da ta yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted