Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin.

Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Tattaunawar ta biyo bayan bukatar shugaba Putin na yiwa shugaba Ramaphosa bayanin shirin zaman lafiya da Ukraine da kuma magance batutuwan da suka shafi moriyar juna.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted