Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza

A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai

A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin.

Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da kada ta bi wannan zabi, wanda zai kara ta’azzara matsaloli a zirin Gaza, tana mai jaddada cewa, tilasta tsugunnar da  Falastinawa a wajen yankunansu ya sabawa dukanin dokoki na kasa da kasa.

Wang ta sake nanata kiranta na “tsagaita bude wuta, da shigar da kayan agaji ba tare da wani cikas ko tarnaki ba, da kuma sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su tun watan Oktoban 2023.”

Ta yi nuni da cewa, batun kafa kasashe biyu ita ce hanya daya tilo ta hanyar samun zaman lafiya mai dorewa, ta hanyar kafa kasar Falasdinu tare da kasar Isra’ila, da zaman lafiya da tsaro a cikin iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.”

Duk da ci gaba da sukar da take yi wa Isra’ila, har yanzu Australia ba ta bi sahun kawayenta na yammacin duniya kamar Canada da Faransa ba wajen bayyana aniyarsu ta amincewa da kasar Falasdinu mai ci cin gashin aknta ba. Duk da haka, ta jaddada cewa “za ta yanke shawara a lokacin da ya dace.”

Kalaman na Wang sun zo ne a matsayin mayar da martani ga wata hira da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi da gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana aniyar Isra’ila na kakaba takunkumin soji a daukacin zirin Gaza. Ya ce, “Tel Aviv na son mika wa dakarun Larabawa yankin gabar tekun don tafiyar da shi,” ba tare da fayyace tsari ko kuma  kasashen da za su shiga cikin shirin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted