Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Boye Barnarta A Zirin Gaza

Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza

Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba

Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata a kan Falasdinawa a zirin Gaza ba, ba tare da gabatar da tuhumce-tuhumce ko cimma matsaya mai kyau ba tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a watan Oktoban shekara ta 2023.

Rahoton ya nakalto Action on Armed Violence yana cewa: gwamnatin mamayar Isra’ila na neman dauke hankalin duniya kan rashin hukunta ta ta hanyar gujewa daukar alhakin manyan laifukan da suka faru a Falasdinu, ciki har da kisan Falasdinawa 112 yayin da suke yin layi don neman garin abinci a watan Fabrairun shekara ta 2024, a hare-haren sama wanda ya kashe Falasdinawa 45 a sansanin Rafah a watan Mayu, da kuma kisan Falasdinawa 31 da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a cikin watan Yuni, duk a kokarin da gwamnatin mamayar Isra’ila take yi na gujewa daukan alhakin kisan kiyashin kan Falasdinawa, duk da duniya ta tabbatar da hakan a watan Yuni.

Rahoton ya tattara kararraki 52 da hukumomin mamayar Isra’ila suka bayyana aniyarsu ta gudanar da bincike ko gudanar da bincike na hakika, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 1,300 da kuma jikkata kusan 1,880. Sai dai yawancin waÉ—annan lamuran ba su haifar da tabbataccen sakamako ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted