Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Abokantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan wata ingantacciyar dabara ce ta nan gaba Ministan harkokin wajen

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Abokantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan wata ingantacciyar dabara ce ta nan gaba

Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Iran da Pakistan za su iya mayar da yankin daga fagen gasa zuwa cibiyar hadin gwiwa, yana mai bayyana hadin kai a fagen yaki da ta’addanci a matsayin wata cikakkiyar bukata. Ya ce, “Lokaci ya yi da za a zurfafa hadin gwiwar tsaro.”

A daidai lokacin da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya kai ziyara birnin Islamabad, ministan harkokin wajen kasar Seyyed Abbas Araqchi, a wata makala da ya buga a jaridar “The News” ta kasar Pakistan mai take “Makomar Gaba” ya bayyana bangarori daban-daban na dangantakar Iran da Pakistan da kuma damar da kasashen biyu ke da su.

A cikin wannan makala, Araghchi ya yi ishara da cewa, daya daga cikin muhimman manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne kulla alaka mai karfi, daidaito da kuma moriyar juna da kasashe makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted