Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa, HKI ba zata iya rayuwa ta kuma aikata abinda take aikatawa a gaza ba, ba tare da tallafin Amurka ba. Don haka Amurka da alhakin duk abinda yake faruwa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Syyid Abdul Malik Badruddin Huthi yana fadar haka a jawabin mako makon da ya saba gabatawa.
Labarin ya kara da cewa kawancen gwagwarmaya a yankin ba zasu ajiye makamansu ba, har zuwa lokacinda aka kawo karshen ta’asan da ke faruwa a Gaza.
Alhuthi ya bayyana haka ne a dai-dai lokacinda, kawancin masu gwagwarmaya, a yankin wato Hizbullah na kasar Lebanon, Gwagwarmayan musulunci a Iraki da kuma JMI da kuma Yemen suke kara tabbarwa ba zasu daina yaki da HKI har zuwa lokacin da aka kawo karshen ta’asar da HKI take yi a gazar.
Daga karshe Sayyid Huthi ya bayyana cewa, banda makamai da kayakin yakin da Amurka take bayarwa har yanzun tana taimakawa HK da goyon bayan siyasa da sauransu.