Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi

Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi

Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi na kasar Mali Husseini Sanou, da ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivlev, inda suka tattauna kan “hadin gwiwa a fannin makamashi, musamman wajen yin amfani da makamashin nukiliya domin ayyukn farar hula.

Taron ya samu halartar wakilan “manyan kamfanonin makamashi na Rasha da ma’aikatun gwamnatin tarayya,” kamar yadda ya zo a cikin wata sanarwa da ma’aikatar makamashi ta Rasha ta fitar a shafinta na intanet, a cewar kafar yada labarai ta African Readings.

Bangarorin biyu sun tattauna kan fagagen da suka yi alkawarin yin aikin hadin gwiwa a fannin hakar albarkatun kasa, binciken sararin samaniya, tsaro ta yanar gizo, da kuma aikin gona,” baya ga hanyoyin da za a bi wajen samar da kayayyakin masarufi a kasar Mali da kasashen Sahel, wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar tsarin ayyukan hadin gwiwa,” a cewar sanarwar ma’aikatar makamashi ta kasar Rasha.

A ziyarar da ya kai birnin Moscow a watan Yunin da ya gabata, shugaban majalisar rikon kwarya a kasar Mali, Janar Assimi Goita, ya amince tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan kafa kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin Mali da Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted