Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki

Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da

Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su shiga yajin aiki amma a safiyar jiya litinin likitocin sun dakatar da ayyuka a dukkan asbitocin gwamnatin Jihar.

A bangaren kasha na jami’ar koyon aikin likita na Jami’ar Lagos marasa lafiya da dama sun fito don ganin likotocinsu amma sai aka fada masu duk sun shiga ya jin aiki. Wanta marasa lafiya wacce taki fadar sunanta ta fadawa Premium times kan cewa ta zo ganin likita amma an ce mata sai ranar 4 ga watan Augusta ta dawo. Kuma kafarta yana mata ciwo sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted