Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin.

Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar.

 A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yanzu yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako.

 An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar Gaza, da hana shigar da madarar jarirai da dukkanin kayan agaji.

Bugu da kari ofishin gwamnatin Gaza din ya kuma kara da cewa; Da akwai wasu kafofi da suke watsa jita-jita da karairayi akan shigar da kayan abinci zuwa cikin yankin na Gaza, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

Haka nan kuma ya yi kira ga mutanen Gaza da kar su yarda da wadannan irin karairayin, wacce manufarta rufe hakikanin laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa.

Har ila yau, ofishin na gwamnatin Gaza ya bukaci ganin dukkanin kasashen duniya ba tare da togiya ba, da su yunkura domin karya killace Gaza da aka yi, da kuma bude kan iyakoki saboda a shigar da madarar da kananan yara za su sha, da kuma abincin da mutane fiye da miliyan 2.4 za su ci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted