Ministan harkokin cikin gida na kasar Masar ya bada sanarwan kissan mutane biyu dauke makamai a birnin Alkahira da kuma farar hula guda a wani sumamen da jami’an tsaron kasar suka kai a wata unguwa a birnin
The Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa jami’an tsaron kasar sun kai sumame a wata unguwa a birnin Alkahira babban birnin kasar inda suka yi musayar wuta da mutane biyu wadanda ake tuhuma da ayyukan da addanci, amma kuma musayar wutan yayi sanadiyyar kashe farar hula guda. Sannan jami’in dansanda guda ya ji rauni.
Labarin ya kara da cewa jami’an yan sanda sun kashe masu dauke da bindigar a unguwar Giza na birnin na Alkahira. Sannan fara hula wanda aka kashe mai wucewa kan titi ne kawai ba abinda ya hada shi yan ta’addan. Labarin ya ce mutanen biyu yan kungiyar ‘Harakat Sawa’ed Misr’ kungiya wacce ta sami asali daga kungiyar yan’uwa musulmi. Wadanda suke adawa da shugaba Abdulfattah Assisi.
Rahoton ya ce jami’an tsaro sun dade suna bin sawon wadan nan yan ta’adda tunda da dadewa. Gwamnatin kasar Masar dai tana daukar kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kasar a matsayin kungiyar yan ta’adda tun shekata 2013M .
Kungiyar dai tana ganin gwamnatin shugaban assisi ya gaza a taimakon da yakamata na bawa gaza, wadanda HKI take masu kissan kiyashi.