Iran da kasashe uku na turai wato Jamus, Faransa da kuma Ingila zasu farfado da tattaunawa a tsakaninsu a mako mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran yace bangarorin biyu sun amince su farfado da tattaunawa kan shirin Nukliyar kasar Iran a mako mai zuwa amma har yanzu basu ayyana lokaci da kuma wurin taron ba.
Tasnim ya bayyana cewa majiyar tawagar tattaunawa ta kasar ta shaida masa kan cewa za’a gudanar da tattaunawar ne a matakin ministocin harkokin waje na kasashen 4, amma basu bayyana wuri da lokaci ba.
Har’ila yau labarin ya bayyan cewa agenda tattaunawar kuma su ne shirin Nukliyar kasar Iran da kuma batun daukewa JMI takunkuman tattalin arziki.