Adaidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 653 ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; yunwa ta kashe Falasdinawa 900, daga cikinsu da akwai kananan yara 71.
Haka nan kuma sanarwar ta ce da akwai wasu falasdinawan 6,000 wadanda suke fama da yunwa, suke neman abinda za su ci.
A cikin kisan kiyashi na bayan nan da ‘yan sahayoniyar su ka yi, wasu falasdianwa 34 sun yi shahada, sai kuma wasu 60 da su ka jikkata sanadiyyar harin da aka kai musu, suna cikin layin gogoriyon neman abinda za su ci.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kuma ce, da akwai kananan yara masu yawa da suke mutuwa sannu a hankali saboda yunwa. Haka nan kuma da akwai wasu mutanen miliyan biyu da yunwar da suke fama da ita ta kai makura.
Ma’aikatar ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi matsin lamba akan HKI ta bari a bude iyaka domin a shigar da kayan agajin da aka girke, kuma masu yawa.