Unrwa Ta Sake Yin Kira Ga HKI Da Ta Bari A Shigar Da Kayan Agaji

Hukumar Agaji ta MDD mai kula da Falasdinu ( Unrwa) ta sake yin kira ga HKI da ta bari a shigar da kayan agijin da

Hukumar Agaji ta MDD mai kula da Falasdinu ( Unrwa) ta sake yin kira ga HKI da ta bari a shigar da kayan agijin da take da su masu yawa a jibge a yankin Arish na kasar Masar.

 Hukumar ta yi wannan kiran ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X tana mai bayyana cewa; tana da abinci mai yawan gaske da zai ishi yankin Gaza har tsawo watanni 3, amma yana cikin dakunan ajiya, an kuma hana shigar da shi.

Yankin Gaza dai yana fuskantar hare-hare na kisan kiyashi da kare dangi daga HKI tun daga 2023, har ya zuwa yanzu babu kakkautawa. A cikin wannan yanakin ne kuma HKI ya hana shigar da kayan agaji da hakan ya jefa mutane cikin matsananciyar yunwa.

A wani hali na rashin tausayi da kuma keta da mugunta, sojojin HKI suna kashe Falasdinawan da suke zuwa cibiyoyin da aka ware da sunan bayar da agaji. Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da aka kashe a cibiyoyin bayar da agaji sun  kai daruruwa.

Su ka kananan yaran da suke mutuwa saboda yunwa suna da yawa.

A yau da yakin Gaza ya cika kwanaki 652, HKI tana ci gaba da tsananta yunwar da mutanen Gaza suke ciki.

Daga safiyar yau Asabar zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada, sun kai 70, daga cikinsu da akwai 36 a filin raba kayan agaji da yaudara.

A filin daga kuwa sojojin HKI sun sanar da cewa biyu daga cikin sojojinsu sun jikkata a yankin Khan-Yunus dake kudancin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted