Shugaban Mabiya Duruz A kasar Lebanon Yace Basa Bukatar Kariyar HKI

Sheikh Sami Abi al-Muna, shugaban kungiyar mazhabar Duruz a kasar Lebanon ya bayyana cewa jama’arsu basa bukatar kariya daga HKI, duk da cewa suna daga

Sheikh Sami Abi al-Muna, shugaban kungiyar mazhabar Duruz a kasar Lebanon ya bayyana cewa jama’arsu basa bukatar kariya daga HKI, duk da cewa suna daga cikin kananan mazhabobin addinin musulunci a kasar ta Lebanon.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abi-Almun yana fadar haka a taron da malamai da shuwagabannin mazhabar suka kira a birnin Beirut babban birnin kasar ta Lebanon a jiya Jumma’a.

Malaman yana magana ne dangane da hare-haren da jiragen yakinta suka kai kan birnin Damash babban birnin kasar Lebanon, da sunan kiare mabiya mazhabar Duruze da suke zaune a yankin Suwaida na kudancin kasar Siriya.

Kuma hakan ya faru ne bayan da aka yi ta fafatawa da mayakan kungiyar ta Duruz da HTS masu mulkin kasar ta Siriya tun farkon wannan shekarar. Bayan wadannan hare-hare dai gwamnatin HTS da ke Damascus ta yarda cewa dususawa a Suwaida sun sami yencinsu daga kasar ta Siriya.

Al-muna ya bayyana cewa abunda HKI ta yi ya bata jama’arsa da tarihinsa. Y ace HKI ta fito da sunan taimakawa Durusawa don aiwatar da shirinta na yayyaka kasar Siriya kamar yadda take so. Har’ila yau yau yace fada da durisawa suka yi da Bedaen a yankin suwaida ya lakume rayukan mutanen da dama. Amma shigar HKI yafi muni a garesu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted