Iran Ta Musanta Zargin Aikawa Huthawan yemen Makamai

Kakakin  ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai ya musanta zargin gwamnatin kasar Amurka na cewa iran ce take bawa mayakan Huthi na yemen makamai,

Kakakin  ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai ya musanta zargin gwamnatin kasar Amurka na cewa iran ce take bawa mayakan Huthi na yemen makamai, wadanda take cillawa kan HKI sannan take tare jiragen ruwan kasuwanci na HKI ta kuma lalatasu ko ta nutsr da su cikin ruwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esmail Baghae yana fadar haka ne a jiya Alhamis ya kuma bayyana zargin ba gaskiya bane, kuma kasar Iran bata barazana ga ko wace kasa a yankin inda banda HKI wacce ta shelanta yaki da kasar.

Ya kuma dorawa gwamnatin kasar Amurka laifin dukkan ta’asan da HKI take aikatawa a wannan yankin. Y ace zangin da takewa JMI don halattawa HKI ci gaba da keta hurumin kasashen yankin da kuma yin abin da ta ga dama a yankin ne.

Y ace idan ba tallafin siyasa da makamai wanda HKI take samu daga Amurka ba, da kuwa ba zata ci gaba da barnan da take yi a wannan yankin ba, musamman a kasashen siriya da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted