A jiya Alhamis an yi jana’izar ‘yan kungiyar Hizbullah 5 da HKI ta kashe a hare-haren bayan nan a yankin Bikaa.
Daga cikin wadanda aka yi jana’izar tasu da akwai Shahid Duraid Nayif al-Attar a garin Sha’ash dake arewacin Bikaa, tare da kai shi makwancinsa na karshe a makabartar shahidai.
A garin Ba’alabak kuwa an yi jana’izar shahid Muhammad Abbas al-khatib, tare da yin bayani daga jagororin Hizbullah a yankin,sannan a karshe aka kai shi makwancinsa na karshe a makabartar shahidai.
A can garin al-Allaq kuwa an yi sahid Hussain Ahmad Kanifan jana’iza, inda mahalarta su ka rika bayar da taken ci gaba da riko da tafarkin gwgawarmaya. An kuma rufe shi a kusa da abokan gwagwarmaya a makabartar shahidai dake garin.
Sai kuma shahid Sayyid Riyad Nasib Haidar Ahmad, wanda aka yi tashi jana’izar a garin “Ra’as Usdha’ a Jubail inda mutanen garin su ka yi alkawalin ci gaba da gwgawarmaya da riko da tafarkin shahidai.
Tare da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki tun a shekarar da ta gabata, sai dai kuma HKI tana ci gaba da kai hare-hare da kashe mutane a cikin kasar ta Lebanon.