Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’I ya tir da kungiyar kasashen Turai kan sabbin takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa daddaikun mutane a kasar .
Baqae ya bayyana haka ne a jawaban da ya gabatar a jiya, yana maida martani kan wannan mataki da kasashen turan suka dauka, sannan ya kara da cewa Eu sun gabatar da hujja wacce bata da wani karfin na daukar wannan matakin kan wasi zababbun Iraniyawa. Sannan ya ce manufarsu ita ce karfafa yan ta’addan wadanda suke renonsu don cutar da JMI da su.
Sannan suna amfani da yan ta’addan don biyan bukatun HKI wacce kowa a duniya ya san cewa kasashen ta yan ta’adda da kuma cutar da kasashen yankin.