A wani bayani da hukumar kididdiga ta kasar Najeriya ta fitar a jiya laraba , ya nuna yadda an sami koma bayan hauhawar kayan masarufi, da a cikin watan Yuni ya kasance da 22.22%. Sai kuma a cikin watan Mayu ya kasance da kaso 22.97%.
A shekarar da ta gabata an sami hauhawar tashin gwauron zabi na kayan masarufi da ya sa rayuwa ta yi tsada.
A lokacin babbar sallar da ta wuce ma dabbobi sun yi tsada sosai, ta yadda yin layya ya ta’azzara ga mutanen da a baya sun saba yi a kowace shekara.
A watan Yuni da ya gabata kuwa an sami karuwar farashin kayan abinci ne da kaso 21.97%, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin.
Sai dai kuma kwararru a fagen tattalin arziki suna cewa har yanzu da akwai sauran tafiya kafin a warware matsin lambar tattalin arziki da mutane suke fama da shi.