Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya yayi kira ga kasashen musulmi su dunkule su hadakansu don fuskantar HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya yayi kira ga kasashen musulmi su dunkule su hadakansu don fuskantar HKI.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban ya na fadar haka a lokacinda yake ganawa ministan harkokin gida na kasar Pakisatan Mohsen Naqvi.

Shugaban ya kara da cewa a cikin wannan halin da ake ciki a yankin Asia ta kudu ba. Don hadin kan musulmi ne zai basu nasara kan HKI.

Shugaban yace HKI tana kokarin raba kan al-ummar musulmi don su kasa yin koma a kissan kiyashi da take yi a kan falasdinawa.

Daga karshe Pezeshkiyan ya gargadi kasashen musulmi, majalisun dokokinsu da jami’an gwamnatocinsu su tsuge dangantakarsu da hki , don taimakawa hadin kan kasashen musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted