Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, yawan sojojin da suke daukar rayukansu da kansu a lokacin da suke kan ganiyar aikinsu, yana karuwa.
Jaridar ta kuma ce, a cikin wannan shekarar ta 2025 kadai adadin sojojin da su ka kashe kawukansu sun kai 15,yayin da a cikin shekarar 2024 bakidayanta sojojin da su ka kashe kansu su ne 21.
Wata majiyar soja ta fada wa jaridar ta ‘yan sahayoniya cewa mafi yawancin wadanda su ka kashe kawukan nasu, sun fuskanci wani yanayi ne da ya yi musu tasiri mai girma.
A cikin makwani daya kadai na bayan nan sojojin da su ka kashe rayukansu sun kai 3.
Radiyon sojojin HKI ya bayyana cewa; sojan da yake kashe kansa a ranar Litinin din da ta gabata, yana a karkashin rundunar “Nahal” wacce take da sansaniya a tuddan Gulan.
A makon da ya shude kuwa wani sojan daga rundunar Gulani wanda shi ma ya yi yaki a Gaza ya kashe kashe kansa a sansanin “Timan dake saharar Naqan.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa daga fara yakin Gaza zuwa yanzu adadin sojojin da su ka kashe kansu sun kai 44,saboda halayyar keta da mugunta da su ka aikata akan Falasdinawa da hakan ya haukata su.