Somaliya: ‘Yan Kungiyar Shabab Sun Shimfidi Iko A Wani Gari Dake Tsakiyar Kasar

Wata majiyar Sojan kasar Somaliya ta bayyana cewa, ‘yan kungiyar al-shabab masu dauke da makamai sun shimfida ikonsu a garin “Tardo” dake gundumar Hiran a

Wata majiyar Sojan kasar Somaliya ta bayyana cewa, ‘yan kungiyar al-shabab masu dauke da makamai sun shimfida ikonsu a garin “Tardo” dake gundumar Hiran a tsakiyar kasar, kuma suna ci gaba da nausawa cikin yankunan kasar.

Jami’in sojan   kasar Somaliya Kaftin Muhammad Abdullah ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Garin Tardo yana a matsayin mahadar dake hada muhimman yanukan kasar, wacce a halin yanzu ya fice daga ikon hukuma, bayan da kungiyar al-shabab ta kori mayakan hauloli dake aiki da hukuma.”

Abdullah ya kuma yi ishara da cewa; kungiyar ta al-shabab tana ci gaba da nausawa cikin wasu yankunan baya da ta shimfida iko a Tardo. Sai dai kuma ya ce, mayakan hauloli ake kira da Makowaisili, suna kara jan damara domin kai farmaki.”

Haka nan kuma ya ce, ya tattauna da mutanen yankin Hiran akan tsarin da za a yi aiki da shi domin sake kwato garuruwan da su ka shiga karkashin ikon al-shaba, tare da jaddada cewa ya zuwa yanzu sun aike da sojoji 100 domin karfafa mayakan dake yankin.

Shi kuwa jagoran haulolin yankin da kuma mayaka, sannan kuma dan majalisa a cikin majalisa gundumar ya ce, kama wannan garin na Tardo da kungiyar Shabab su ka yi, zai sa su sami saukin kutsawa cikin garuruwa da dama. Da akwai iyalai 12,500 da su ka yi hijira bayan kutsen kungiyar ta al-shabab.

Tun a farkon wannan shekarar ta 2015 ne dai kungiyar ta al-shabab take samun nasarar kutsawa cikin garuruwa, bayan da a baya ta yi rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted