Iran Ta Yi Tir Da Takunkuman Tattalin Arzikin Da Amurka Ta Dorawa Ma’aikaciyar MDD

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai yayi tir da gwamnatin Amurka kan takunkuman da ta dorawa Francesca Albanese jami’a Ta musamman a hukumar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai yayi tir da gwamnatin Amurka kan takunkuman da ta dorawa Francesca Albanese jami’a Ta musamman a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD wacce take aikin tattara bayanai dangane da yakin da ke faruwa a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Bakaei yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa ; Ba wanda ya isa ya rufe bakin gaskiya. Ya ce gwamnatin kasar Amurka ta dorawa malama Francesca Albanese takunkumi ne saboda fadin gaskiya. Saboda tsayawa kan cewa Natanyahu yana aikata kisan kiya shi a gaza. Ya na kashe yara kanan da mata. Kuma ta sha bada shawarwari ga hukumar kare hakkin bil’adama na MDD na a kori HKI daga hukumar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted