Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; An Mika Batun Hakin Gwiwa Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA Ga Kwamitin Kolin Tsaron Kasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An mika fayil ɗin haɗin gwiwa tare da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ga kwamitin koli na tsaron ƙasa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a wata ganawa da jakadun kasashen waje da na kasa da kasa cewa: Iran bangare […]
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran

Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Sanarwar […]
Ma’aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon Ta Yi Furuci Da Hasarar Da Harin Iran Ta Janyo Mata

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi furuci da cewa hakika an lalata sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid na Qatar Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Sean Parnell ya yi furuci da cewa: Makami mai linzami na Iran da aka kai hari da shi kan sansanin jiragen sama na Al Udeid da ke Qatar, a […]
Gwamnatin Mauritaniya Ta Karyata Rahoton Cewa Shugaban Kasarta Ya Gana Da Netanyahu

Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da […]
Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra\ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa A Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Gaza, kuma Falasdinawa da dama sun yi shahada Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da ruwan bama-bamai a yankuna daban-daban na zirin Gaza a rana ta 117 da yakin ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama. A cewar majiyoyin […]
Iran Tana Nazarin Sakon Amurka Na Bukatar Farfado Da Tattaunawa Shirin Makamashin Nukliya Na kasar

Mai bawa jagoran Juyin Juya halin musulunci Imam Sayyid Ali Khamina’i, shawara Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana nazarin sakon gwamnatin Amurka na bukatar a farfado da tattaunawar shirin makamashin Nukliyar kasar tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Dr Larijana yana cewa gwamnatin kasar Iran tana shakkar […]
NYT: Natanyahu Yana Tsawaita Yaki A Gaza Don Ci Gaba Da Kasancewa Kan Iko A HKI

Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya […]
Kyautar ‘Jakadan Abota’ Na Kasar China Ya Shiga hannun Iran

Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu. Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin […]
Iran Ta Yi Tir Da Takunkuman Tattalin Arzikin Da Amurka Ta Dorawa Ma’aikaciyar MDD

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai yayi tir da gwamnatin Amurka kan takunkuman da ta dorawa Francesca Albanese jami’a Ta musamman a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD wacce take aikin tattara bayanai dangane da yakin da ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Bakaei yana fadar […]
Lavrov: Shuwagabannin Kasashen Yammacin Turai Suna Son Shiga Yaki Da Rasha

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar […]
Jamhuriyar Nijar Da China Sun Kusa Warware Sabanin Dake Tsakaninsu Akan Batun Man Fetur

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ce, wata majiya mai karfi a jamhuriyar Nijar ta ce; An kusa kusa kawo karshen sabanin dake tsakanin gwamnatin jamhuriyar Nijar da kamfanonin kasar China da suke aiki a fagen hako da tace man fetur, bayan da bangarorin biyu su ka yi nisa a tattaunawar da suke yi. Sauyin da […]
Fiye Da Falasdinawa 60 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i Kadan

Ma’aikatar kiwon Lafiya ta Falasdinawa ta sanar a jiya Juma’a cewa; An kai gawawwakin shahidai 61 zuwa asibitocin yankin Gaza, a cikin sa’oi 24. Ya zuwa yanzu adadin mutanen Gaza da su ka yi shahada tun daga 2023 sun kai 57,823, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 137,887. Su kuwa Falasdinawan da […]
Iran: Goyon Bayan Shugaban Gwamnatin Jamus Ga ‘Yan Sahayoniya, Yin Tarayya Ne A Fada Da Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya […]