Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s).
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Matasan da su ka yi watsi da duniya su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu ne mu kare ta.”