An Fara Gudanar Da Jana’izar Shahidan Yakin Kwanaki 12 A nan Tehran

A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana

A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali har zuwa dandalin yenci dake tsakiyar birnin na Tehran . Ana dauke da gawakin shahidan rufe da tutan Iran a cikin akwatuna.

Daga cikin manya-manyan bakin da suka halarci tattakin har da shugaban kasa Dr Masoud Pezeshkiyan da kuma wasu ministocinsa . A ranar 13 ga watan Yuni ne HKI ta fara kaiwa kasar Iran yaki inda ta kashe mutane da dama daga daga ciki har da manya-manyan kwamandojojin sojojin kasar da masana fasahar Nukliya da kuma sauran mutanen gari maza da mata da yara. Muta ne kimani 600 ne suka yi shahadi a cikin yakin kwanaki 12 da HKI ta kai hare-haren.

Bayan yan sa’o’I ne sojojin kasar ta Iran suka fara maida martani da dandazon makamai masu linzami. Wadanda suka lalata biranen HKI, har sai da suka nemi tsagaita wuta. Kafin karshen yakin dai sojojin Iran sun kai dandazon makamai har sau 22. An tsagaita wuta ne a ranar 24 ga watan Yuni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted