Arakci:  Idan Aka Kai Iran Bango Za Ta Fito Da Hakikanin Karfin Da Take Da Shi

Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su

Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei.

Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan  Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba, idan kuwa har aka kai ta bango ta za ta bayyana hakikanin karfin da take da shi.

A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar ta Amurka ya yi maganganu na rashin labadi akan jagoran juyin musulunci, sannan kuma ya kara da cewa, zai sake kawo wa Iran  hari idan ta koma tace sanadarin uranium.

Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha jaddada cewa ba za ta ja da baya ba akan hakkinta na tace sanadarin Uranium da cin moriyar fasahar Nukiliya ta hanyoyin zaman lafiya.

Arakci ya kuma ce; Idan har shugaban kasar ta Amurka da gaske yake akan batun tattaunawa da kai wa ga cimma wata yarjejeniya, to ya daina yin Magana da harshe na rashin ladabi akan jagoran juyin musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted