Sojojin Iran Sun Bada Sanarwan Cewa Babu Iyaka Na Wuraren da Zasu Kai Hari A HKI

Manya-manyan jami’an sojojin kasar Iran sun bada labarin cewa a halin yanzu babu wasu kebabbun wuraren da zasu kaiwa hare-hare a HKI,. Wato hare haren

Manya-manyan jami’an sojojin kasar Iran sun bada labarin cewa a halin yanzu babu wasu kebabbun wuraren da zasu kaiwa hare-hare a HKI,. Wato hare haren zasu game ko ina a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin na fada a safiyar yau Jumma’a bayan hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu wurare a kasar wadanda suka kai ga shahadar manya-manyan Jami’an sojojin kasar da kuma wasu masana fasahar Nukliya.

Labarin ya kara da cewa hare-haren maida martanin da sojojin JMI zasu kai zai sauya al-amuran tsaro a gabas ta tsakiya, musamman ganin irin asarorin da HKI ta yiwa kasar.

Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu muna makokin Janar Janar Hussain Salami, da Janar Muhammad Bakira da Janar Ghukam Ali Rasheet amma kuma zamu daukin fansar jininsu nan da yan sa’aoi masu zuwa.

 Labarin ya kammala da cewa hare-haren HKI a safiyar yau Jumma’a a nan Tehran da wasu wurare a kasar yayi sanadiyyar shahadar wasu fararen hula maza da mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted