Wagner ta kawo karshe kasantuwarta a Mali bayan fiye da shekaru uku

Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a

Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka.

“Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare kasarsu.

Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a kasar,” in ji Wagner.

Kasar Mali, da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012, kuma sojojin dake mulki a kasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulda.

A farkon wannan shekarar, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, da sojoji sukayi juyin mulki, sun fice daga kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka, inda suka  kafa wata sabuwar kungiya mai suna AES.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted