Iran Ta Sami Muhimman Bayanai Na Sirri Akan Shirin Nukiliyar HKI

Tashar talabijin din ‘almayadin” ta ambato wata majiya ta Iran tana cewa; Jami’an leken asirin kasar sun sami muhimman byanai akan Shirin Nukiliyar HKI. Majiyar

Tashar talabijin din ‘almayadin” ta ambato wata majiya ta Iran tana cewa; Jami’an leken asirin kasar sun sami muhimman byanai akan Shirin Nukiliyar HKI.

Majiyar ta kara da cewa; Jami’an leken asirin Iran sun iya isa ga wadannan muhimman bayanan masu yawan gaske tare da yin jigilarsu zuwa cikin kasar Iran. Daga cikin bayanan da akwai wadanda su ka shafi shirye-shiryen da ‘yan sahayoniyar suke aiwatarwa na Nukiliya da kuma cibiyoyin Nukiliyar.

Majiyar ta kara da cewa;  jami’an leken asirin na Iran sun iya kai wa ga wadannan bayanan tun shekarun  da su ka gabata, kuma saboda yawan bayanan da kuma hanyoyin shigo da su cikin Iran ne ya sa ba a bayyana shi ba sai yanzu.

Haka nan kuma majiyar ta ce bayanan sun hada hotuna na cibiyoyin Nukiliyar HKI da kuma bidiyo da suka bukaci lokaci mai tsawo na yin nazarinsu.

Majiyar almayadin ta ce; Abu ne mai yiyuwa mutanen da HKI ta bayyana cewa ta kama su a cikin kwanakin bayan nan, suna da alaka da wadannan bayanan da su ka shiga hannun Iran.

Har ila yau, tashar talabijin din ta kuma ambaci cewa; Fitar da wannan sanarwar a wannan lokacin yana da nashi muhimmanci bisa la’akari da halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted