Fransa Ta Kira Yi Kasashen Turai Da Sake Bitar Alakarsu Da “Isra’ila”

Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi

Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza da kuma hana shigar da kayan agaji.

 Matakin na Faransa dai ya biyo bayan na kasashen Spain, Ireland da kuma Holland, da suke son ganin an gudanar da bincike akan ko hare-haren Gaza din sun karya wani sashe na yarjejeniyar tasu. A karkashin yarjeniyoyin tarayya a tsakanin turai da HKI da akwai batun kare hakkin bil’adama.

Tun a cikin watan Yuni na 2000 ne nahiyar turai din ta kulla yarjejeniyar ayyuka a tsakaninta da HKI a fagage da dama, da hakan ya bai wa Tel Aviv fifiko na musamman a cikin kasuwannin turai. Harkokin kasuwanci a tsakaninsu ya kai dala biliyan 46.8 a 2022.

Ministan harkokin wajen Faransa  Jean-Noël Barrot ya bayyana cewa; Saboda matsayar Isra’ila akan gaza, ya zama wajibi a yi bitar alakarta da tarayyar turai.

Barrot ya bayyana tsananta hare-haren akan Gaza da kuma hana shigar da kayan abinci da cewa ” Ba abu ne da za a lamunta da shi ba.”

Haka nan kuma ya bayyana hare-haren na Isra’ila da cewa; cin zarafin Karaman dan’adam ne da kuma keta dokokin kasa da kasa, kuma yana cin karo da tsaron Isra’ila da Faransa ta yi alkawalin karewa,to amma duk abinda mutum ya shuka shi zai girba.

Gabanin Faransa, Faransa, kasar Holland ta yi kira irin wannan na yin bitar alaka da Isra’ila,wacce ministan harkokin wajen na Faransa ya ce, yana goyon baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted