Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin na cewa tattaunawar ta yi amfani.”
Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine a kan wata yarjejeniya “game da samar da zaman lafiya a nan gaba.”
“Rasha da Ukraine za su fara tattaunawa nan take domin tsagaita bude wuta,” in ji Trump.
A cewar wata majiya kusa da tattaunawar da ke gudana, shugaban fadar White House ya tuntubi Volodymyr Zelensky “na ‘yan mintoci kadan” kafin kiran Putin.
“Daidaita” dangantaka, musayar fursunoni, Iran da Gabas ta Tsakiya na daga cikin batutuwan da aka tattauna.
Mr. Putin ya yaba da shawarwarin da ake yi tsakanin Washington da Tehran kan shirin nukiliyar Iran da aka faro ta hanyar shiga tsakani na Oman.”