Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo Janar Muhammad Bakiri ya ce; Alakar soja da kuma ta tsaro a tsakanin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma Pakistan tana kara daukaka kuma za ta ci gaba.
Manjo janar Muhammad Bakiri wanda ya isa birnin Islamabad ya kuma ce:
“ A cikin shekara daya da ta gabata, mun ga sauye-sauyen da su ka faru a cikin wannan yankin, da Iran da Pakistan suke ciki, wanda yanki ne mai muhimmanci.”
Babban hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran yana ziyarar kwanaki biyu ne a Pakistan, a karkashin amsa kiran takwaransa na kasar Janar Asim Munir. A yayin wannan ziyarar zai gana da manyan jami’an sojan kasar da kuma shugaban kasa da fira minista, da ministan tsaro.
Kasashen Iran da Pakistan suna da iyakoki masu tsawo, sannan kuma suna kokarin tabbatar da tsaro a cikinsu.
Da akwai kyakkyawar alaka tsakanin Iran da makwabciyata Pakistan a cikin fagage da dama.