An Kashe Sojojin  HKI 2  Da Jikkata Wasu 10 A Kudancin Kasar Lebanon

Kafafen watsa labarun HKI sun ce an kashe sojojinsu 2 a yayin da wasu 10 su ka jikkata a fafatawa da suka yi da ‘yan

Kafafen watsa labarun HKI sun ce an kashe sojojinsu 2 a yayin da wasu 10 su ka jikkata a fafatawa da suka yi da ‘yan gwgawarmaya a kudancin kasar Lebanon. Majiyar ta ce a jiya Asabar ce sojojin biyu su ka halaka.

Asibitin soja na “Rambam”  dake birnin Haifa, ya sanar da cewa an kai masa mutane 3 da su ka jikkata sa’oi kadan da su ka gabata, kuma an dauko su ne daga kan iyakar kasar da kasar Lebanon.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fafatawa a filin daga a tsakanin mayakan Hizbullah da kuma sojojin mamayar HKI, musamman a cikin garuruwan Khayam, Kafar-Killa, Deir- Mimas, Shama’a da kuma Biyadha.

Dakarun na Hizbullah su na amfani da makamai masu linzami akan sojojin mamayar, sannan kuma suna yakarsu gaba da gaba.

A safiyar yau Lahadi ma, mayakan Hizbullah sun harba jirage marasa matuki zuwa cikin yankunan daban daban  a arewacin HKI.

Sanarwar da Hizbullah ta fitar ta ce, ta harba jiragen yaki marasa matuki zuwa Nahariyar Kafar-Fardim da kuma Afan-Manahim.

An ji karar jiniyar gargadi ta na kadawa a cikin yankin Jalil-Ta yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments