Iran ta yi gargadi game da kudurin nuna mata adawa daga bangaren IAEA

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah wadai da sabon takunkumin da kasashen Turai suka kakabawa kamfanonin jiragen sama da na jiragen ruwa na

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah wadai da sabon takunkumin da kasashen Turai suka kakabawa kamfanonin jiragen sama da na jiragen ruwa na kasar, yana mai jaddada cewa duk wani mataki na nuna adawa da Tehran a taron kwamitin gudanarwa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA mai zuwa zai kara dagula lamarin.

Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noël Barrot a wannan Laraba, yayin da suke musayar ra’ayi kan shawarwarin nukiliya da kuma halin da ake ciki a yankin a baya-bayan nan.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi Allah wadai da kakkausar murya da cewa, matakin da kasashen Turai suka dauka na sanya sabbin takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan abin da suka yi ikirarin cewa Tehran ta samar da kayan aikin soji zuwa ga Rasha  don amfani da shi a yakin Ukraine, wannan mataki na tsokana ne domin kuwa babu wata hujja da kasashen turai suke da ita kan hakan, in ji shi.

Araghchi ya kuma yi kakkausar suka ga matakin da kasashen turai  uku na Jamus, Faransa da Birtaniya suka dauka na gabatar da wani kuduri na nuna adawa da Iran a taron kwamitin gwamnonin hukumar IAEA a ranar Laraba.

Ministan harkokin wajen na Iran ya ce “Wannan matakin da kasashen Turai uku suka dauka ya sabawa kyakykyawan yanayi da aka samu a huldar da ke tsakanin Iran da Hukumar.”

A yayin da yake ishara da ci gaban yankin da ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Labanon da kuma kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza, Araghchi ya yi tir da goyan bayan kisan gillan Isra’ila a kan al’ummar Gaza da kasashen turai suke nunawa, ko dai ta hanyar taimaka ma Isra’ila da makamai wajen aiwatar da waannan kisan kiyashi, ko kuma ta hanyar kin daukar matakan da suka dace domin ladabtar da ita.

Tattaunawar ta wayar tarho na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Birtaniya, Faransa da Jamus, tare da goyon bayan Amurka, ke ci gaba hankoron ganin an aiwatar da wani kuduri kan Tehran a kwamitin IAEA a zaman wanann wannan mako.

Kudurin dai zai dorawa Iran alhakin abin ya kira rashin hadin kai daga bangaren Iran Iran ga hukumar IAEA dangane da  shirinta na nukiliyar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments